‘Yan takara 17 ne waɗanda suka haɗa da maza 16 da mace ɗaya ke fafatawa a zaɓen domin neman maye gurbin gwamna mai ci a halin yanzu wato Godwin Obaseki. / Hoto: Arise

Hukumar zaɓen Nijeriya INEC ta soma tattara sakamakon zaɓen gwamnan Jihar Edo wanda aka gudanar a ranar Asabar.

Shugaban Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Minna, Farfesa Faruk Adamu Kuta shi ne babban baturen zaɓen jihar.

Tun da farko hukumar ta INEC ɗin ta sanar da cewa ta ƙaddamar da sashen duba sakamakon zaɓe ta intanet domin bayar da damar saka aika sakamakon rumfunan zaɓe cikin gaggawa.

‘Yan takara 17 ne waɗanda suka haɗa da maza 16 da mace ɗaya ke fafatawa a zaɓen domin neman maye gurbin gwamna mai ci a halin yanzu wato Godwin Obaseki.

Sai dai daga cikin ‘yan takarar 17, mutum uku ne za a iya cewa za su fi fafatawa a tsakaninsu.

‘Yan takarar ukun waɗanda suka fi shahara sun haɗa da Asuerinme Ighodalo na Jam’iyyar PDP sai Monday Okpebholo na Jam’iyyar APC da kuma Olumide Osaigbovo Akpata na Jam’iyyar Labour Party.

Rahotanni daga jihar ta Edo sun tabbatar da cewa an tsaurara tsaro a ofishin hukumar zaɓe wato INEC reshen jihar.

A daren jiya gwamnan na Edo mai barin gado Godwin Obaseki ya kai ziyara ofishin na INEC da tsakar dare, wanda har hakan ya jawo ‘yar ƙaramar hatsaniya, inda ‘yan sanda suka buƙaci ya bar ofishin INEC ɗin.

Sai dai daga baya gwamnan ya bayyana cewa ya je ofishin na INEC ne sakamakon an hana wakilan PDP shiga ɗakin tattara sakamakon zaɓe

TRT Afrika