Hukumar zabe mai zaman kanta a Nijeriya ta ayyana Umaru Ahmadu Fintiri a matsayin wanda ya ci zaben gwamnan Jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin kasar.
Da yake jawabi a yayin sanar da sakamakon, Baturen Zaben Farfesa Muhammed Mele ya ce Fintiri, wanda shi ne gwamnan jihar mai ci, ya samu kuri'a 430,861 yayin da Sanata Aisha Binani ta APC ta samu kuri'a 396,788.
An sanar da sakamakon zaben ne a ranar Talata da yamma cikin tsauraran matakan tsaro.
A watan jiya INEC ta ayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba.
A ranar Lahadi aka fara ce-ce-ku-ce a kasar bayan da wani Kwamishinan zabe, Hudu Yunusa Ari, ya ayyana Sanata Binani a matsayin wacce ta yi nasara, ta yanayin da ya sha bamban da dokar zabe.
Jim kadan bayan hakan ne aka ga Sanata Binani a wani bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta tana jawabin murnar nasararta.
Wannan lamari ya janyo tashin hankali inda wasu bata-gari suka tasar wa babban kwamishinan zabe na kasa na INEC, a zaton shi ne wanda ya sanar da sakamakon, suka ci zarafin sa ta hanyar yi masa duka.
Bayan hakan ne INEC ta fitar da sanarwar cewa wannan sakamakon da aka fada ba daidai ba ne, inda ta ce za a fitar da sahihin sakamako ta hanyar da ta dace.
A ranar Talata ne kuma aka wayi gari INEC din ta bai wa rundunar 'yan sandan Nijeriya umarnin tuhumar Hudu Ari wanda ya sanar da sakamakon farkon, da har ya zama sanadin cin zarafin kwamishinan.
Kazalika INEC ta sha alwashin gano wadanda suka aikata wannna laifi tare da gurfanar da su a gaban kuliya.