A halin yanzu Jam’iyyar EFF ta ce a shirye take domin ta tattauna da ANC domin yin haɗaka. / Hoto: Reuters

Hukumar Zaɓen Afirka ta Kudu (IEC) ta sanar da cewa za ta saki sakamakon zaɓen 29 ga watan Mayu da misalin 6:00 na yamma agogon ƙasar a yau Lahadi.

Ganin cewa an tattara sama da kaso 99 cikin 100 na ƙuri’un ƙasar, jam’iyya mai mulki a ƙasar ta African National Congress ANC ta samu kaso 40.2 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa a zaɓen ƙasar, inda ta rasa rinjaye a majalisar ƙasar a karon farko a tarihi.

Jam’iyyar adawa ta ƙasar ta Democratic Alliance DA ita ce ta zo ta biyu da kaso 21.8 na ƙuri’u sai kuma jam’iyyar tsohon shugaban ƙasar Jacob Zuma wato uMkhonto weSizwe MK ta samu kaso 14.6 cikin 100 na ƙuri’un.

Sai kuma Jam’iyyar Economin Freedom Fighters Party EFF ta zo ta huɗu da kaso 9.4 na ƙuri’u.

A halin yanzu Jam’iyyar EFF ta ce a shirye take domin ta tattauna da ANC domin yin haɗaka.

Zuma ya soki zaɓen

Tuni Jacob Zuma ya yi kira da a ɗage sanar da sakamakon zaɓen inda ya ce akwai wurare da dama da aka samu cikas a yayin zaɓen.

A yayin da yake hira da ‘yan jarida a garin Midrand da ke lardin Gauteng a ranar Asabar, Zuma ya ce: “Muna buƙatar lokaci (domin a magance ƙorafinmu), kada wanda ya kuskura ya sanar da sakamakon zaɓe gobe (Lahadi).

Ina sa ran duk wani wanda ya san abin da yake yi yana jin me muke cewa. Kada ku soma rikici a inda babu rikici.” Zuma ya yi zargin cewa an yi maguɗin zaɓe domin ANC ta samu nasara.

TRT Afrika