Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC) ta ba da umarnin kama Edmond Beina, wanda ake zargi da jagorancin wata kungiyar 'yan bindiga a Jumhuriyar Afirka ta Tsakiya.
Ana zargin Edmond Beina da aikata laifukan yaƙi da kuma miyagun laifuka, ciki har da kisan kiyashi da kisan-kai da fyade, da kuma zalunci da ya aikata Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a shekarar 2014.
Umarnin kamun, wanda aka yi tun shekarar 2018 amma aka bayyana shi kwanan nan, ya yi zargin cewa Beina ya jagoranci hare-hare kan Musulmi farar-hula a yammacin kasar.
A wani ɓangare kuma, an zargi ƙungiyarsa da bazama cikin wani ƙauye, inda suka kashe gomman mazaje da yara maza.
Shekarun yaƙi
Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta yi fama da yaƙi tun shekarar 2013, lokacin da mayaƙan Seleka suka ka kori shugaban ƙasar na wancan lokacin, Francois Bozize daga karagar mulki.
'Yan bindiga da ke hamayya da 'yan tawayen sun mayar da martani, inda suka ƙaddamar da hare-hare kan Musulmi farar-hula da ke zama a babban birnin ƙasar na Bangui, lamarin da ya sa Musulman tserewa.
Masu gabatar da ƙara sun yi zargin cewa Beina na da hannu a aikata laifukan a ƙauyen Guen a yammacin ƙasar, daga watan Fabrairu zuwa watan Afrilun shekarar 2014, ciki har da kashe Musulmi farar-hula.
Ya kuma jagoranci sauran mayaƙa da suka aikata laifuka, a cewar takardar umarnin kama shi.
Farar-hula da aka kashe
A wani ɓangaren kuma, masu gabatar da ƙara sun yi zargin cewa Beina da mayaƙansa sun afka cikin gidan wani shugaban al'ummar Musulmi a ƙauyen Guen, inda 'yan gudun hijira mata da yara 300 ke fakewa.
"Beina ya rarraba 'yan ƙauyen gida-gida da ƙarfin bindiga kuma ya umarci mazaje da yara maza su kwanta a ƙasa. Sannan Beina ya harbe Musulmi maza da yara da bindigar Kalashnikov, inda ya ƙarar da jigidar alburushi biyu a kansu," in ji takardar umarnin kama shi.
"Beina ya umarci mutanensa su ƙarasa duk wanda bai mutu ba a harin," in ji takardar, tana mai ƙarawa da cewa aƙalla Musulmi 42 mazaje da yara maza ne aka kashe a harin.
A halin yanzu dai akwai wasu mutum uku da ake yi wa shari'a a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, kan rawar da suka taka a rikicin ƙasar da ke tsakiyar Afirka.