“A wannan lamari ne jami’an kwastam biyu Alhaji Kabiru Shehu da Abdullahi Muhammad suka rasa rayukansu,” in ji sanarwar. Hoto: NCS

Hukumar hana fasa-kauri ta Nijeriya ta tabbatar da mutuwar wadansu jami’anta guda biyu, sakamakon kashe su da aka yi a Jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin kasar.

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Juma’a, hukumar ta kwastam ta ce wasu ‘yan bindiga ne suka bude wa tawagar jami’an nata wuta, har su biyu, inda kuma suka rasu.

“A ranar Alhamis da misalin karfe 1:28 na rana ne wata tawagar jami’an kwastam da ke shiyyar Kebbi, da suke bakin aikinsu na tsayar da ababen hawa don bincikensu, a kan titin Bunza zuwa Dakingari da Koko, bayan samun wasu sahihan bayanai, sai wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne a wata motar Toyota Corolla launin ruwan toka suka bude wa jami’an wuta."

“A wannan lamari ne jami’an kwastam biyu Alhaji Kabiru Shehu da Abdullahi Muhammad suka rasa rayukansu,” in ji sanarwar.

Tuni aka yi jana’izar mamatan kamar yadda addinin Musulunci ya tsara. Sanarwar ta kara da cewa hukumar kwastam ta kaddamar da bincike don gano wadanda suka aikata laifin, domin su fuskanci shari’a.

Sannan hukumar ta ja hankalin jama’a da su bayar da bayanai kan zirga-zirgar duk wanda ake zargi da fasa-kauri, ko aikata miyagun laifuka.

A karshe kuma, hukumar ta jajantawa iyalan mamatan tare da yi musu ta’aziyya.

TRT Afrika da abokan hulda