Hukumar Kwastam a Nijeriya ta bayyana cewa za ta yi gwanjon lita 15,325 na man fetur ga jama’a domin saukaka wahalhalun sufuri a lokutan bukukuwan ƙarshen shekara.
Shugaban rundunar daƙile fasa kwabrin man fetur ta ‘Operation Whirlwind’ na Nijeriya, ACG Hussein Ejibunu ne ya sanar da hakan yayin ganawa da manema labarai da aka gudanar a Kwalejin Horar da Kwastam da ke Ikeja, a ranar Asabar, 21 ga Disamba, 2024.
Ya kuma yi karin haske game da kama jarka 613 na man fetur da jami’ansu suka kama a kan hanyar Legas-Ogun da kudin su ya kai N27,565,000.
"An fara gudanar da wannan aiki tun ranar 27 ga watan Mayun 2024 kuma an samu sakamako mai kyau,” in ji shi.
Mista Ejibunu ya bayyana cewa kamar yadda Kwanturola Janar na hukumar ya umarta, na a yi gwanjon fetur ɗin da aka ƙwace, ofishin mai ba da shawara kan harkokin shari’a ya kamalla da batun hukuncin kotu da kuma dukkan matakan shari’a.