Hukumar kashe gobara ta Ghana ta ce a shekarar 2023, ta samu kiran neman dauki na bogi sau 656, 951 daga jama’ar kasar.
Kamfanin dillancin labarai na Ghana ya ruwaito hukumar tana bayyana haka a bikin cikar hukumar shekara 60 da kafuwa.
Hukumar ta bayyana cewa ta samu wadannan kiraye-kirayen tsakanin watan Janairu zuwa Nuwambar 2023, lamarin da ya jawo hukumar ayyuka suka yi mata yawa matuka.
Mista Julius Kuunuor, wanda shi ne shugaban hukumar, ya bayyana cewa kiraye-kirayen bogi ya saka rayukan jami’an kai agajin a cikin hatsari da kuma jawo asarar man fetur.
“Idan muka rinka yin kiraye-kiraye na bogi, za mu rinka saka rayuwar ma’aikata a cikin hatsari da kuma jawo asarar fetur,” kamar yadda ya kara da cewa.
Mista Kuunuor ya bukaci jama’ar kasar da su guji wannan dabi’a sakamakon hukumar ba za ta lamunci irin haka ba a shekarar 2024.
Hukumar ta tabbatar da cewa gobara ta ragu da kaso 4.92 cikin 100 a watanni 11 na 2023, inda aka samu gobara sau 5,256 idan aka kwatanta da 5,530 a 2022.
Sakamakon muhimmancin aikin hukumar kashe gobara ta Ghana, ko a bara sai da gwamnatin kasar ta bayar da umarnin daukar mutum 2,000 aikin kashe gobara domin kara samun sauki.
Haka kuma gwamnatin ta yi alkwarin cewa gwamnatin kasar za ta karo motocin kwana-kwana 200