A kowace shekara dubban mutane ke tafiya Aikin Hajji daga Nijeriya. / Hoto: Kaduna State Pilgrims

Hukumar Alhazan Nijeriya NAHCON ta fitar da sabon kudin kujerar Aikin Hajjin 2024.

A kwanakin baya ne dai hukumar ta saka naira miliyan hudu da dubu ɗari biyar a matsayin kafin alƙalami, sai dai a sanarwar da ta fitar ta ce ta yi niyyar barin wannan kuɗin a matsayin kuɗin Hajji amma hakan ba zai yiwu ba sakamakon karewar darajar naira.

A halin yanzu hukumar ta ce maniyyata daga kudancin Nijeriya za su biya N4,899,000 a matsayin kuɗin Aikin Hajji sai kuma waɗanda suka fito daga arewacin ƙasar za su biya N4,699,000, sai kuma waɗanda suka fito daga jihohin Yola da Maiduguri su biya N4,679,000.

A cikin sanarwar da mai magana da yawun hukumar Fatima Sanda Usara ta fitar, ta bayyana cewa hukumar ta bayar da shawara ga maniyyata su biya sauran kuɗin da ya rage na Aikin Hajjin zuwa Litinin 12 ga watan Fabrairu domin bai wa hukumar damar tura kuɗaɗen Aikin Hajjin.

Wannan ƙarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar karyewar darajar naira a Nijeriya, lamarin da ya jawo matsin tattalin arziki a ƙasar.

TRT Afrika