Hedkwatar Tsaron Nijeriya ta tabbatar da kisan sojojin ƙasar 22 tare da jikkata da dama a wani harin ƙunar-baƙin-wake da mayaƙan Boko Haram suka suka kai musu a yankin da ake kira Timbuktu Triangle da ke tsakanin jihohin Borno da Yobe.
Mai magana da yawun Hedkwatar Tsaron Nijeriya, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi da maraice.
Ya ce lamarin ya faru ne ranar 24 ga watan Jahairu yayin da sojojin Nijeriya suka ƙaddamar da hare-hare a sansanonin mayaƙan ƙungiyar da zummar murƙushe gyauron 'yan Boko Haram.
Manjo Janar buba ya ce dakarunsu na Operation Haɗin Kai sun ƙaddamar da hare-haren ne tun daga ranar 16 zuwa 25 ga watan Janairu inda suke ƙokarin kammala kawar da mayaƙan Boko Haram da suka rage a yankin.
“Dakarunmu sun fafata sosai da 'yan ta'adda a yayin da suke karkaɗe ɓurɓushinsu inda suka kashe 'yan ta'adda fiye da 70 ciki har da manyan 'yan ta'adda uku. Kwamandojin 'yan ta'addan da aka kashe sun haɗa da: Talha (Kwamandan 'yan Ta'adda na Musamman), Mallam Umar (Kwamandan Gudanarwa na 'yan Ta'adda), da Abu Yazeed (Kwamandan Birget na 'yan Ta'adda),” in ji sanarwar.
Buba ya ce, “Lokacin kai wannan samame, 'yan ta'adda sun yi amfani da abubuwa da ke fashewa da 'yan-ƙunar-baƙin-wake domin daƙile dakarunmu."
Ya ƙara da cewa hakan ne ya yi sanadin mutuwar dakarun Nijeriya 22 tare da jikkata gommai.
“Abin baƙin ciki, an kashe dakarunmu 22 tare da jikkata da dama a fagen-daga. Don haka, muna kira ga kafofin watsa labarai su guji wallafa sunayensu dakarunmu da aka kashe har sai mun sanar da iyalansu,” in ji Manjo Janar Buba.