Hedkwatar Tsaro ta Nijeriya ta musanta labaran da ake yaɗawa kan cewa an naɗa muƙaddashin shugaban sojin ƙasa na Nijeriya.
Hakan na zuwa ne bayan wasu kafofin watsa labarai na Nijeriya sun ruwaito mai magana da yawun sojin ƙasa na Nijeriya Manjo Janar Onyema Nwachukwu na cewa sakamakon hutun da Janar Lagbaja ya tafi, Manjo Janar Abdulsalami Bagudu Ibrahim ne ke aiki a madadin Lagbaja.
Sai dai a wata sanarwa da mai magana da yawun hedkwatar tsaro na Nijeriya Birgediya Janar Tukur Gusau ya fitar, Janar ɗin ya ce a yi watsi da duk wasu rahotanni da ke nuna cewa an bayar da shugaban riƙon ƙwarya na soji.
“Shugaban Sojin Ƙasa na Nijeriya Laftanar Janar Taoreed Lagbaja na gudanar hutunsa na shekarar 2024. Ana gudanar da aikin sojin Nijeriya bisa ƙwarewa haka kuma duka shugabannin sojin na gudanar da ayyukansu bisa kundin tsarin mulkin Nijeriya.
“Manjo Janar Abdulsalam Bagudu Ibrahim, wanda shi ne shugaban tare-tsare da dabaru, na bayar da bayanai ga shugaban sojin ƙasa kamar yadda tsarin soji ya tanada,” in ji sanarwar ta Tukuar Gusau.
“Hedikwatar tsaro na buƙatar masu yaɗa jita-jita su guji yin hakan nan take. Shugaban Sojin Nijeriya yana nan cikin ƙoshin lafiya kuma zai koma bakin aiki da zarar ya kammala hutunsa,” in ji Tukur Gusau.
Haka kuma hedikwatar tsaron ta buƙaci kafofin watsa labarai da su rinƙa tabbatar da labari daga hukumomin da suka dace kafin su watsa wa jama’a.