Dubban mutane ke mutuwa sakamakon hatsarin mota a Nijeriya a duk shekara. Hoto/Reuters

Hukumar kiyaye hadura ta Nijeriya ta ce mutum 4,387 ne suka mutu sakamakon hatsarin mota daga Janairu zuwa Yunin 2023 a fadin kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ya ruwaito jami’in wayar da kan jama’a kan ka’idojin hanya ACM Bisi Kazeem na cewa akasarin wadannan haduran sun faru ne sakamakon tukin ganganci.

“Daga Janairu zuwa Yuni, jimillar mutum 4,387 ne suka rasu sakamakon hatsarin mota. Hukumar ta kuma tabbatar da samun raunuka 14,108 daga haduran da aka yi a lokutan.

“Wadannan haduran sun faru ne sakamakon tafiyar dare da gajiya da rashin bin hanyar da ta dace, da tukin ganganci da amfani da tayoyin da suka lalace da kuma gudun-wuce-sa'a.

“Kuma kun san mutanenmu ba sa aiki da dare, shi ya sa wadannan direbobin suke amfani da rashin mu a kan tituna da daddare domin karya dokar titi,” in ji shi.

Mista Kazeem ya bayyana cewa daya daga cikin dalilan da suka sa ake yawan samun haduran har da rashin kwarewa da kuma karancin horo na wasu direbobi.

TRT Afrika da abokan hulda