Hukumomi a Nijeriya sun tabbatar da mutuwar akalla mutum talatin da shida sakamakon hatsarin kwale-kwale a jihohin Neja da Adamawa.
Gwamnatin jihar Neja da ke tsakiyar Nijeriya ta tabbatar da rasuwar akalla mutum 26 sakamakon kifewar kwale-kwale a karamar hukumar Mokwa ranar Lahadi.
Kakakin gwamnatin jihar Bologi Ibrahim ya ce mutane da dama sun bata sakamakon hatsarin kwale-kwalen wanda ke dauke da fiye da mutum 100, cikinsu har da mata da kananan yara.
A cewarsa, mutanen suna kan hanyarsu ce ta zuwa gona yayin da lamarin ya faru.
"An tabbatar da mutuwar akalla mutum ashirin da shida, yawancinsu mata da kananan yara, yayin da aka ceto fiye da 30, kuma yanzu haka gamayyar ‘yan sanda da masunta da jami’an hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja suna ci gaba da neman wadanda lamarin ya rutsa da su,” in ji shi.
A nata bangaren, hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Nijeriya ta tabbatar da mutuwar akalla mutum goma a hatsarin kwale-kwalen da ya faru a Kogin Njuwa da ke karamar hukumar Yola ta Kudu.
Shugaban hukumar Aminu Sulaiman ya ce an ceto mutum 10. Kwale-kwalen da ya kife ranar Juma’a yana dauke da akalla mutum 23 da ke kan hanyarsu ta zuwa kasuwa, in ji shi.
Nijeriya ta dade tana fama da hatsarin kwale-kwale, wanda hukumomi suka ce yana faruwa ne sakamakon daukar mutane fiye da kima da kuma rashin ingancin kwale-kwalen.
A watan Yulin da ya gabata, fiye da mutum 100 ne suka mutu sakamakon kifewar da kwale-kwalen da suke ciki ya yi a jihar Neja.