Mutane 23 ne suka halaka, yayin da mutane 40 suka jikkata. / Hoto: AP

Wata haɗakar ƙungiyar masu sa-kai don aikin ceto a Sudan ta ce sojojin Sudan sun kai hari ta sama kan wata kasuwa a birnin Khartoum, inda suka halaka mutane 23.

"An tabbatar da mutuwar mutum 23 kuma wasu 40 sun samu raunuka" sannan an kai su asibiti bayan wani "harin soji ta sama ranar Asabar kan babbar kasuwar" kudancin Khartoum, cewar ƙungiyar Emergency Response Rooms a wallafarta ta shafin Facebook ranar Lahadi.

Kasuwar da aka kai wa harin tana kusa da babban sansanin rundunar Rapid Support Forces (RSF) da ke babban birnin, wadda da ita ne sojin Sudan suke fafata yaƙin basasa, wanda ya halaka dubban mutane.

A cewar Majalisar Ɗinkin Duniya, yaƙin na sama da watanni 16 a Sudan ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane 20,000.

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ce Sudan tana fama da matsanancin rikici, sannan matakin tagayyarar jama'a ya kai maƙura, ga shi kuma ba a samun wani babban yunƙurin warware rikicin.

Sudan ta faɗa yaƙi ne a Afrilun bara lokacin da dangantaka ta yi tsamari tsakanin rundunar sojin ƙasar da rundunar ɗaukin gaggawa, kuma yaƙi ya ɓarke tsakaninsu a faɗin ƙasar.

TRT World