Hukumomin lafiya a Sudan sun ce wani mummunan hari da aka kai ta sama a birnin Omdurman ya kashe akalla mutum 22.
Ma'aikatar lafiyar kasar ta ce an kai harin ne ranar Asabar a yankin da mutane ke zama a birnin wanda ke makwabtaka da Khartoum, babban birnin kasar.
Wata sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta kara da cewa harin ya yi sanadin raunata mutane da dama.
Kasar ta Sudan ta fada yaki ne ranar 15 ga watan Afrilu sakamakon rikicin neman iko tsakanin shugaban kasar Abdel Fattah al-Burhan da mataimakinsa, Mohamed Hamdan Dagalo, wanda kuma shi ne shugaban runduna ta musamman ta Rapid Support Forces (RSF).
Rundunar ta RSF ta rika kai hare-hare a Khartoum da Omdurman da kuma Bahri, inda su ma sojojin kasar ke kaddamar da hare-hare ta sama a-kai-a-kai.
A kwanakin baya bayan nan, yakin ya fi zafi a Omdurman domin kuwa RSF na amfani da yammacin birnin a matsayin wata hanya da take wucewa da karin kayan aiki da take tahowa da su daga Darfur, inda ta fi karfi.
Hare-haren da aka kai, ciki har da luguden wutar da aka yi ranar Juma'a da daddare, sun mayar da hankali ne a ginin kafar watsa labaran kasar da ke gabashin Omdurman.Kazalika an kai hare-hare da daddare a kudanci da gabashin Khartoum.
Wata sanarwa da rundunar sojin kasar ta wallafa a Facebook ta ce dakarunta na musamman sun kashe "sojojin 'yan tawaye" akalla 20 sannan sun lalata makamansu.
Kawo yanzu an kashe akalla mutum 1,133 a rikicin, a cewar ma'aikatar lafiyar kasar, tana mai cewa yakin ya yi kamari a babban birnin kasar da yankin Kordofan da na Darfur, inda ya rikide ya zama rikicin kabilanci a Yammacin yankin.
Fiye da mutum miliyan 2.9 sun tsere daga gidajensu sakamakon yakin, ciki har da mutum kusan 700,000 da suka ketara zuwa kasashen da ke makwabtaka.