Rundunar sojin Nijeriya ta nemi maƙwabciyarta Nijar da ta kama wani shugaban 'yan bindiga da ta ce tana nema ruwa a jallo a ƙasar. kamar yadda mai magana da yawun hedkwatar tsaro ya faɗa a ranar Alhamis.
Mai magana da yawun Hedkwatar Tsaron Edward Buba ya ce Halilu Sububu ɗan ƙasar Nijar kuma shi ne babban mai samar da makamaki a Nijeriya daga masu sayar da su a Libiya.
A wata sanarwa, Buba ya ce Sububu yana kuma aiki a wani wajen haƙar zinare a Zamfara, ɗaya daga cikin jihohin da ke fama da matsalar satar mutane.
"A lokacin da dakaru suka kusa cim masa, sai ya tsallaka kan iyakar Jamhuriyar Nijar don neman mafaka," in ji Buba.
'Kama shi'
"A wannan lokacin, muna bi ta hanyoyin da suka dace dona kira ga hukumomin Nijar da su kama shi, tare da hukunta shi kan wannan ta'asa da ya aikata."
A watan Nuwamban 2022, sojojin Najeriya sun ce sun kashe Halilu Sububu tare da wasu shugabannin kungiyoyin masu garkuwa da mutane, amma Buba ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Alhamis cewa "ba sabon abu ba ne a ce mutane daban-daban suna da suna iri daya ko da a tsakanin 'yan ta'adda."
Rundunar sojin ta ce ‘yan bindigar da ke da alaƙa da ƙungiyar Sububu sun kashe mutum 19 a wani ƙauye a makon da ya gabata a wani hari da suka kai a Zamfara.
Yankin arewa maso yammacin Nijeriya ya shafe shekaru yana fama da matsalar ‘yan fashi, lamarin da ya yi sanadin kashe dubban mutane.