An bai wa Louise Aubin umarnin barin kasar cikin awa 72.

Gwamnatin sojin Nijar ta nemi babbar jami'ar Majalisar Dinkin Duniya a kasar da ta fice daga Nijar nan da awa 72, a cikin wata sanarwa da AFP ta gani wacce sojojin suka fitar a ranar Laraba.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Nijar a sanarwar wacce ke dauke da kwanan watan ranar Talata, ta ce gwamnati ta bai wa Louise Aubin, babbar jami'ar ayyukan jinkai ta MDD, "da ta dauki dukkan matakan da suka dace don ficewa daga Nijar cikin awa 72."

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres yana matukar bakin cikin korar jami'arsu daga Nijar, in ji mai magana da yawunsa Stephane Dujarric, wadda ta tabbatar da cewa an bai wa Aubin awa 72 ta fita daga Nijar.

Dujarric ta ce matakin zai kawo tsaiko a ayyukan da Majalisar take yi a Nijar, ko da yake ta jaddada cewa "Majalisar Dinkin Duniya ba za ta gaza ba wajen ci gaba da zama da kuma bayar da jinkai ga al'ummar Nijar".

An nada Aubin, 'yar kasar Canada, a kan wannan mukamin ne a watan Janairu na 2021.

A ranar Talata, Faransa ta fara janye dakarunta daga Nijar tare da kwashe jami'an diflomasiyyarta bayan makonni ana cacar baki tsakanin shugabannin sojin da suka kwace mulki a ranar 26 ga watan Yuli.

AFP