Sojoji sun kifar da gwamnatin Mali a juyin mulkin da suka yi a shekarar 2021, sannan suka ƙi cika alƙawarin da suka ɗauka na gudanar da zaɓe a watan Fabrairu, inda suka ɗage ranar gudanar da zaɓen har sai abin da hali ya yi. /Hoto: Fadar Shugaban Mulkin Sojin Mali

Gwamnatin sojin Mali ta ɗage haramcin da ta sanya kan harkokin siyasar ƙasar don tabbatar da doka da oda, a cewar majalisar ministoci a taron da ta yi ranar Laraba da maraice.

A watan Afrilu ne aka sanar da dakatar da duk wani taro ko harkoki na siyasa, kwanaki kaɗan kafin soma tattaunawar zaman lafiya a ƙasar da ke yankin Sahel wadda ke fama da hare-haren masu tayar da ƙayar baya, wacce kuma sojoji suke mulkarta tun daga watan Agustan 2020.

"Wannan mataki da gwamnati ta ɗauka ya ba ta damar murƙushe duk wata barazana da ake yi ga tsaron ƙasa," in ji sanarwar da majalisar ministocin ta fitar.

Ta ƙara da cewa yanzu gwamnati ta ɗage duk wani haramci da ta sanya game da harkokin siyasa a yuƙurinta na aiwatar da shawarwarin da aka bayar a taro kan zaman lafiya da aka yi daga ranar 13 ga watan Afrilu zuwa 10 ga watan Mayu.

Sojoji sun kifar da gwamnatin Mali a juyin mulkin da suka yi a shekarar 2021, sannan suka ƙi cika alƙawarin da suka ɗauka na gudanar da zaɓe a watan Fabrairu, inda suka ɗage ranar gudanar da zaɓen har sai abin da hali ya yi.

A wancan lokacin, 'yan siyasa da ƙungiyoyin fararen-hula sun caccaki sojojin sannan suka yi kira a koma mulkin farar-hula ba tare da ɓata lokaci ba.

Sojoji sun yi juyin mulki sau takwas a ƙasashen Yammaci da Tsakiyar Afirka tun daga watan Agustan 2020 inda suka kifar da gwamnatoci a Mali, Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar, kuma suka ayyana yaƙi da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya da ke da alaƙa da al Qaeda.

Reuters