Shugabannin sojojin kasar Gabon, wadanda suka hambarar da Shugaba Ali Bongo Ondimba a watan Agusta, sun sanar da cewa za a gudanar da zabe a watan Agustan shekarar 2025 a ƙarƙashin wani jadawalin da zai fara hasashen tattaunawar kasa.
"Agustan 2025: zaɓe da kuma kawo ƙarshen miƙa mulki," kamar yadda mai magana da yawun gwamnatin ya faɗa a gidan talabijin na ƙasar a ranar Litinin.
Za a gabatar da wa'adin lokacin ga wani taron ƙasa wanda ya ƙunshi dukkan "muhimman masu ruwa da tsaki" na kasar, wanda aka tsara yin sa a watan Afrilun 2024
Gwamnatin riƙon ƙwarya ta kuma sanar da cewa za a gabatar da daftarin kundin tsarin mulki a karshen watan Oktoba na shekarar 2024, kuma za a gudanar da zaben raba gardama kan amincewa da shi a tsakanin Nuwamba zuwa Disamba 2024.