Rahotanni daga Jihar Ribas da ke kudu maso kudancin Nijeriya na cewa an rushe ginin majalisar dokokin jihar da ke Fatakwal babban birnin jihar.
An gudanar da rusau din ne a daidai lokacin da gwamnan jihar Siminalayi Fubara yake gabatar da kasafin kudin 2024 a gidan gwamnatin jihar ga Kakakin Majalisar Jihar Edison Ehie da makarrabansa.
A ranar Talata ne Kotun Jihar Ribas ta tabbatar da Edison Ehie, wanda abokin gwamnan jihar ne a matsayin halastaccen kakakin majalisar.
Wasu daga cikin kafofin watsa labarai na Nijeriya sun wallafa bidiyon motocin buldoza da ke rugurguza ginin.
Sai dai a sanarwar da kwamishinan watsa labarai na jihar Joseph Johnson ya fitar, ya ce ya zama tilas gwamnati ta yi kwaskwarima ga ginin majalisar sakamakon gobarar da ta faru a ranar 30 ga watan Oktoba.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake kara samun tsamin dangantaka tsakanin gwamnan Jihar Ribas Siminalayi Fubara da kuma tsohon gwamnan jihar Nyesom Wike.