Tuni hukumar NSIB ta ce ta soma bincike kan lamarin. / Hoto: Reuters

Hukumar da ke bincike kan hatsarin jiragen sama da ƙasa da na ruwa da motoci a Nijeriya NSIB ta ce ta soma gudanar da bincike kan wani ƙaramin jirgin sama da ya samu matsala a hanyarsa ta zuwa Ghana daga Nijeriya.

Jirgin mai lambar rajista 5NKAL mallakar kamfanin jiragen sama na Fly Bird ya tashi ne daga filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja zuwa babban filin jirgin Kotoka da ke Accra babban birnin Ghana.

Binciken wucin-gadi da hukumar ta NSIB ɗin ta gudanar ya gano cewa duka injinan jirgin biyu sun samu matsala wanda hakan ya tilasta masa juyawa ya koma Abuja domin sauka.

A sanarwar da daraktar watsa labarai ta hukumar Bimbo Olawumi Oladeji ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana cewa jirgin yana ɗauke da mutum huɗu ne waɗanda suka haɗa da ma’aikatan jirgin uku da kuma fasinja ɗaya.

Ta bayyana cewa jirgin na a saman iska a mataki na 240 yana hanyar zuwa mataki na 280 suka samu rahoton inji na biyu ya samu matsala inda direbobin jirgin suka buƙaci za su juya domin komawa Abuja.

“Nan take aka ba su damar yin hakan inda aka amince da jirgin ya yi tafiya a mataki na 190,” in ji Bimbo.

“A lokacin da jirgin ke yin ƙasa, sai injin ɗin na biyu ya daina aiki baki ɗaya a mataki na 230,” kamar yadda ta ƙara bayyanawa.

A cewarta, ko da jirgin ya isa Abuja a lokacin yana kan ƙafa 5,000 tsakaninsa da ƙasa sai direbobin jirgin suka sanar da sun shiga halin ko-ta-kwana sakamakaon sun rasa inji na farko shima baki ɗaya, inda a ƙarshe sun samu nasarar sauka a filin jirgin Abuja.

Sanarwar ta tabbatar da cewa babu wanda ya ji rauni a cikin jirgin kuma hukumar ta NSIB za ta ci ga a da gudanar da bincike kan lamarin.

TRT Afrika