“Don haka muna kira ga jama’a da su yi watsi da wannan ƙaryar,” in ji sanarwar Mohammed Idris. Hoto: MOI

Gwamnatin Nijeriya ta ce ba ta da niyyar kafa sansanin sojojin ƙasashen waje a cikin ƙasar, kamar yadda Ministan Watsa Labarai Mohammed Idris ya faɗa a wata sanarwa.

“Gwamnatin tarayya na sane da ƙaryar da ake ta yaɗawa da ke cewa ana tattaunawa tsakanin gwamnatin tarayyar Nijeriya da wasu ƙasashen ƙetare kan batun zaman sansanonin sojojin ƙasashen waje a kasar.

“Don haka muna kira ga jama’a da su yi watsi da wannan ƙaryar,” in ji sanarwar.

A kwanakin baya ne wasu rahotanni suka rinƙa yawo waɗanda ke nuna cewa Shugaban Nijeriya Tinubu na shirin amincewa da ƙasashen Amurka da Faransa su mayar da manyan sansanoninsu Nijeriya bayan ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso sun yi hannun riga da su.

Bayan hakan ne sai wasu daga cikin fitattu kuma masana daga arewacin Nijeriya suka aika wasiƙa ga Shugaba Tinubu da Majalisar Tarayya, wadda aka rubuta ranar 3 ga watan Mayun 2024, suna buƙatar gwamnatin ta guji ɗaukar wannan matakin.

Amma sanarwar Minista Idris ta jaddada cewa babu wata tattaunawa da Gwamnatin Tarayya take yi da kowace ƙasar waje.

"Ba mu samu wata buƙata daga kowace ƙasa ba, kuma babu wani shiri da muke yi na na shirin kafa sansanon sojin kasashen waje a Nijeriya ba."

Gwamnatin Nijeriyar ta ce tuni take samun hadin kan kasashen waje wajen tunkarar kalubalen tsaro da ake fama da shi, kuma Shugaban Ƙasa ya ci gaba da jajircewa wajen zurfafa wannan ƙawance, da nufin cimma manufofin tsaron kasa na Ajandar Sabunta Fata.

TRT Afrika
Muna amfani da ka’idojin yanar gizo. Muna son ku san cewa idan kuka ci gaba da amfani da wannan shafin, kun amince da wadannan ka’idojin.Ka’idoji
Na amince