Gwamnatin Jamhuriyar Nijar da wani kamfanin ƙasar Canada, Zimar, sun sa hannu kan wata yarjejeniya domin gina sabuwar matatar mai a yankin Dosso da ke makwabtaka da Benin.
Gwamnatin ta Nijar da kamfanin mai na Zimar sun saka hannu kan wannan yarjejeniya a ranar Alhamis 24 ga Oktoba inda yarjejeniyar ta ƙunshi batun yadda za a tsara aikin ginin matatar da kuɗin da za a kashe wurin ginin da yadda matatar za ta yi aiki da kuma kula da ita bayan kammala gininta.
Sabuwar matatar da za a gina a Nijar ɗin ana sa ran za ta rinƙa tace ganga 100,000 a kullum.
Mataimakin Shugaban Mulkin Sojin Nijar Salifou Mody wanda shi ne ya bayar da sanarwar ya bayyana cewa wannan aikin zai kasance babbar dama ga Nijar haka kuma sakamakon wannan yarjejeniya da ƙasar ta ƙulla da kamfanin na Canada, ‘yan ƙasar na Nijar za su samu ayyuka da kuma dama iri daban-daban.
Mista Mody ya kuma bayyana cewa idan Nijar ta rinƙa tace man da take da shi da kanta, hakan zai taimaka wurin rage dogaro da shigar da mai ƙasar da kuma haɓaka tattalin arziƙin ƙasar.
Nijar ta zama ƙasar da ke samar da mai a shekarar 2011 bayan gano mai a Goumeri da Sokor da Agadi da ke yankin Diffa.
A Janairun 2012, Nijar ɗin ta ƙaddamar da matatar manta ta farko wadda ke da ƙarfin tace ganga 20,000 a duk rana a yankin Zinder.
A watan Janairun bana, ƙasar ta soma fitar da ɗanyen manta zuwa kasuwannin duniya ta hanyar wani bututun mai wanda ke da nisan kilomita 2,000, wanda ya tashi tun daga Nijar ɗin zuwa cikin Benin.
Ana kallon wannan matakin da Nijar ɗin ta ɗauka a matsayin ci gaba ta ɓangaren tattalin arziƙinta da kuma rage dogaro wurin shigar da mai cikin ƙasarta.