Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta dakatar da watsa shirye-shiryen kafar watsa labarai ta BBC a ƙasar har tsawon wata uku.
Wata sanarwa da ta fito daga ofishin Ministan Watsa Labarai na Jamhuriyar Nijar, Sidi Mohamed Raliou, ta ce an dakatar da watsa duka shirye-shiryen BBC kai-tsaye da na abokan hulɗarta na ƙasar da suka haɗa da R&M da Saraounia da Anfani har tsawon wata uku.
Gwamnati ta ce an ɗauki matakin ne saboda yadda kafar ta BBC ta watsa bayanan 'ƙarya' waɗanda za su iya kawo matsala ga kwanciyar hankali a ƙasar, da kuma dakushe karsashin dakarun ƙasar.
A makon nan ne dai BBC ta bayar da rahoton cewa ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya sun kashe dakarun sojin Nijar 90 a fafatawar da suka yi, rahoton da gwamnatin ƙasar ta musanta.
Kazalika gwamnatin ta Nijar ta ce za ta gurfanar da gidan rediyon Faransa (RFI) a gaban kotu bayan ta zarge shu da neman haddasa fitina tsakanin al'umma da “zummar haifar da kisan ƙare-dangi.”
Sai dai a ranar Larabar da ta gabata Rundunar Sojin Nijar ta musanta harin, inda ta bayyana rahotannin wannan ta'asa a matsayin "kalmomi mara tushe".
Tsawon shekaru Nijar -- tare da makwabtanta biyu Burkina Faso da Mali -- na fama da tashe-tashen hankula na masu iƙirarin jihadi.
A kwanakin baya ƙasashen sun kafa ƙungiyar Sahel Alliance wadda ta shafi inganta tattalin arziki da tsaron ƙasashen.