Gwamnan Jihar Katsina da ke arewacin Nijeriya Dikko Radda ya bayar da umarnin rufe dukkan makarantun kowon kiwon lafiya masu zaman kansu da ke faɗin jihar tare da soke lasisinsu.
Mai bai wa gwamna shawara kan harkokin lafiya, Umar Mammada, ya sanar da wannan mataki ranar Litinin yayin tattaunawa da manema labarai a birnin Katsina.
Gwamnan ya ɗauki matakin ne bayan wani bincike da Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta gudanar da ya nuna makarantun ba su da inganci sannan da dama daga cikinsu ba su da rijista, lamarin da ya tayar da hankalin gwamnati.
Mammada ya ce a shekarun baya-bayan, jihar ta Katsina ta samu ƙaruwar makarantun koyar da harkokin kiwon lafiya masu zaman kansu, waɗanda da dama daga cikinsu ba su da rajista kuma ba su da inganci.
“Ko da yake mun san muhimmiyar rawar da makarantun kiwon lafiya masu zaman kansu suke takawa wajen tabbatar da lafiyar al'umma, amma yana da muhimmanci mu tabbatar da ingancinsu domin kare lafiyar al'ummarmu," in ji Mammada.
Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar za ta samar da tsari mai inganci da zai tabbatar da ƙwarewar irin waɗannan makarantu kafin a ba su damar ci gaba da horar da masu neman ilimin kiwon lafiya.
Jihar Katsina na cikin jihohin Nijeriya da ke fuskantar ƙalubale a fannin kiwon lafiya da tsaro kuma gwamnatin jihar ta sha alwashin shawo kan matsalolin, abin da ya sa masana suka yaba mata kan ɗaukar wannan mataki.