Abba Gida-Gida ya zamo mutum na farko da aka dauki bayanansa aka dora a kan manhajar tsarin.

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da manhajar daukar bayanan ma’aikatan gwamnati da ƴan fansho da ƴan siyasa wajen biyansu albashi a tsarin nan na IPPIS.

Tsarin IPPIS tsari ne da gwamnatin tarayyar Nijeriya ta daɗe tana amfani da shi wajen biyan ma’aikatanta, inda ake ɗaukar bayansu ciki har da zanen yatsun hannu, da nufin rage rashin gaskiya da wasu ke yi na yin aiki a hukumomin gwamnati daban-daban suna karɓar albashi fiye da ɗaya.

A sanarwar da mai magana da yawun gwamnan Jihar Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ranar Talata, Gwamna Abba Gida-Gida kamar yadda aka fi saninsa, ya ce ya bijiro da wannan tsari ne don tabbatar da gaskiya da rashin rufa-rufa da ƙeƙe-da-ƙeƙe wajen tafiyar da al'amuran gwamnati.

Gwamnan ya ƙaddamar da tsarin da aka bai wa suna Kano Integrated Personal and Payroll Information System (KIPPIS) ne a wajen taron Majalisar Zartarwa karo na 12 da aka yi a fadar gwamnatin jihar.

Abba Gida-Gida wanda ya zamo mutum na farko da aka dauki bayanansa aka dora a kan manhajar tsarin, ya ce za a yi amfani da shi ne a duka matakin jiha da na ƙananan hukumomi "don bin tsarin sha'anin kuɗi da duniya ke kai a yanzu."

Gwamnan ya nei mambobin kwamitin ƙaddamar da tsarin KIPPIS da su tabbatar da cewa sun ɗauki bayanan dukkan ma'aikatan gwamnati da ƴan fanshi da masu riƙe da muƙaman siyasa don samun nasarar tsari a faɗin jihar.

Kazalika Babban Akawun jihar Alhaji Abdulkadir Abdussalam, ya ce za a tabatar da cewa ba a samun matsaloli ba a wajen bin tsarin KIPPIS ta kowane fanni da suka haɗa da rage kuɗaɗen mutane.

TRT Afrika