Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan dokar yin gwajin lafiya kafin aure, wacce take umartar dukkan masu niyyar yin aure da su yi gwaje-gwajen kafin su zama ma’aurata.
Wannan doka na zuwa ne a lokacin da ake ta yawan kiraye-kiraye ga al’umma da su dinga yin gwaje-gwajen lafiya ga duk masu niyyar aure, don a rage samun yawaitar wasu cututtukan da suka gallabi jama’a, waɗanda za a iya guje musu ta hanyar gano su da wuri.
Dokar wadda za ta fara aiki ranar 13 ga watan Mayun 2024, ta bayyana cewa duk wanda aka samu da laifin saɓa wa tanadinta, to ya aikata laifi, kuma idan aka same shi da laifi, zai iya fuskantar tarar biyan Naira dubu ɗari biyar har tsawon shekaru biyar.
Sa hannun gwamnan kan dokar na nufin daga yanzu babu wani aure da za a ɗaura shi a Kano ba tare da gabatar da sakamakon gwajin lafiya na rukunin jini ‘genotype’ da ciwon hanta hepatitis B and C, da cutar HIV/AIDS da sauran cututtuka masu alaƙa, in ji sanarwar da daraktan watsa labarai Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanya wa hannu.
“Dokar ta zama wajibi ne don a rage yawan haihuwar yara da cututtuka masu hadari irin su sikila da HIV/AIDS da hepatitis,” in ji sanarwar.
Gwamnatin ta ƙara da cewa “Wannan tsari ya yi daidai da muradun gwamnan Jihar Kano na bunƙasa da samar da kyakkyawan yanayi ga harkar lafiya, don rage matsalolin lafiya da ake fama da su.”
Har ila yau, dokar ta haramta nuna wariya ko ƙyama ga mutanen da ke da HIV/AIDS da cutar sikila da hepatitis, da kuma wasu cututtukan.
Kare martabar aure
A yayin da yake sa hannu kan dokar, Gwamna Abba Gida-Gida kamar yadda aka fi saninsa da shi, ya ce maƙasudin samar da ita shi ne tabbatar da martabar aure a jihar Kano da tabbatar da haihuwar ‘ya’ya masu lafiya, ba tare da wata cuta da za ta yi wa rayuwarsu barazana ba.
Gwamnan ya ce “Ya zama wajibi ga duk wanda ke da niyyar yin aure ya yi gwajin cutar HIV, Hepatitis B da C, genotype, da duk wani gwajin da ya dace kafin aure.
“Bugu da ƙari kuma, dokar ta haramta yin duk wata yarjejeniya ta aure ga mutanen da ke shirin yin aure ba tare da gabatar da takardar shaidar gwaji daga wata cibiyar lafiya da gwamnati ta amince da ita ba,” ya ƙara da cewa.