Ministan Sadarwa da Fasahar Zamani na Ghana, Samuel Nartey George, ya bayar da umarni a rufe gidajen rediyo bakwai a ƙasar kan dalilan tsaron ƙasa da saɓa ƙa’idojin watsa labarai.
A umarnin da ministan ya bayar a ranar Talata, 18 ga Fabrairun 2018, ya buƙaci Hukumar Sadarwa ta Ghana ta aiwatar da umarnin nan take ga gidajen rediyon da lamarin ya shafa.
A wani saƙo da ministan ya wallafa a shafinsa na X, ya bayyana cewa an rufe gidan rediyo ɗaya bisa dalili na tsaro sai kuma gidajen rediyo shida kan dalilin watsa shirye-shirye a kan mitocin rediyo waɗanda ba a amince da su a hukumance ba waɗanda aka gano bayan binciken da aka gudanar.
Gidan rediyon da aka rufe sakamakon dalilin tsaron ƙasa shi ne Gumah FM da ke a Bawku.
Sai kuma gidajen rediyon da aka rufe bisa dalilin saɓa ƙa’ijojin watsa labarai sun haɗa da Fire Group of Companies da ke Sunyani mai watsa shirye-shirye kan 90.1MHz, sai Zar Consult Limited da ke Tamale mai watsa shirye-shirye kan 89.7MHz.
Haka kuma akwai Abochannel Media Group da ke Adidome mai watsa shirye-shirye kan 105.7MHz da Okyeame Radio Limited da ke Bibiani mai watsa shirye-shirye kan 99.7MHz sai kuma Mumen Bono Foundation da ke Techiman mai watsa shirye-shirye kan 99.7MHz da kuma Osikani Community FM da ke Nkrankwanta mai watsa shirye-shirye kan 99.7MHz.
Ya bayyana cewa bayan dakatar da gidajen rediyon, za a ɗauki mataki a kansu nan ba da jimawa ba.
Ministan ya kuma ƙara jaddada aniyarsa ta ƙara sa ido kan watsa shirye-shirye tare da buƙatar duka kafafen watsa labarai su bi ƙa’idojin da aka gindaya musu.