Gwamnatin Chadi ta karbe iko da kadarorin kamfanin mai na ExxonMobil

Gwamnatin Chadi ta karbe iko da kadarorin kamfanin mai na ExxonMobil

Kamfanin ExxonMobil ya shafe gomman shekaru yana harkokin mai da makamashi a Yammacin Afirka
Kamfanin ExxonMobil ya sayar wa kamfanin Savannah Energy hakkin gudanar da ayyukansa kan dala miliyan 407 Photo/AA

Shugaban kasar Chadi na mulkin soja Mahamat Idriss Deby ya saka hannu kan wata doka a ranar Juma’a wadda ta mallaka ilahirin kadarorin kamfanin mai na Exxon Mobil ga gwamnatin Chadi.

Dokar ta bayyana cewa duka kadarori da damar kasuwanci da kuma damar jigilar mai na kamfanin a Chadi a halin yanzu duk sun zama na kasa.

Daga cikin kadarorin da kamfanin yake da su sun hada da jarin kamfanin a bututun mai na sama da kilomita 1,000 wanda ya taso daga Chadi zuwa Kamaru zuwa Tekun Gulf na Guinea inda ake amfani da bututun wurin fitar da mai.

Shugaban kasar “ya saka hannu kan dokar don aiwatar da mayar da duka kadarorin kamfanin Esso Exploration and Production da kuma Esso Pipeline Investments Companies,” in ji wata sanarwa.

Kamfanonin na Esso duk suna karkashin Exxon Mobil. Wannan duk na zuwa ne bayan kamfanin na ExxonMobil ya sayar da hakkin gudanar da ayyukansa a Chadi da Kamaru a watan Disamba ga wani kamfanin Birtaniya wanda ke aikin makamashi da mai a Afrika wato Savannah Energy kan dala miliyan 407.

Gwamnatin sojin Chadi ta kalubalanci wannan cinikin. Ministan man fetur da makamashi na Chadi Djerassem Le Bemadjiel ya bayyana cewa an cimma matsaya kan wannan lamari mai sarkakiya bayan kamfanin Exxon Mobil ya yi watsi da sharuddan da gwamnati ta bayar kan yarjejeniyoyi da dama da aka saka wa hannu.

Esso-ExxonMobil ya shafe gomman shekaru yana aiki a Yammacin Afirka. A makon da ya gabata, kamfanin Savannah Energy ya ce zai je gaban kotu kan lamarin inda yake cewa matakan da gwamnatin Chadi ta dauka sun saba wa yarjejeniyar kasa da kasa.

Kamfanin na Savannah yana da hannun jari na kashi 40 cikin 100 na aikin mai na Doba a kudancin Chadi, wanda yake da rijiyoyin mai bakwai da suke samar da jumullar gangar danyen mai 28,000 a duk rana.

AA