Gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso ta ce ta daƙile "yunƙuri da dama na wargaza ƙasar" wanda wani babban jami'in soji da ya mulki ƙasar ta yammacin Afirka ya jagoranta.
"Mun yi nasarar daƙile yunƙuri da dama na wargaza ƙasar nan," a cewar Ministan Tsaro Mahamadou Sana a wata sanarwa da ya karanto a gidan talbijin na ƙasar ranar Litinin da tsakar dare.
Ya yi zargin cewa Laftanar Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba, wanda aka kifar da gwamnatinsa a 2022, ya jagoranci "sojoji wajen wannan yunƙuri na kifar da gwamnati".
Sana ya ƙara da cewa an kama mutane da dama bisa hannu a yunƙurin kifar da gwamnatin, ciki har da Ahmed Kinda, tsohon kwamandan rundunar tsaro ta musamman ta ƙasar.
Damiba ya ƙwace mulki a ƙasar Burkina Faso a watan Janairun 2022 a juyin mulkin da ya yi wa zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Roch Marc Christian Kabore.
Sai dai watanni takwas bayan haka, kyaftin Ibrahim Traore mai shekara 34 ya kifar da gwamnatin Damiba.
Bayan juyin mulkin ne, Traore ya kori dakarun Faransa daga ƙasar sannan ya sha alwashin kawar da ƙungiyoyin da ke iƙirarin jihadi waɗanda suka shiga ƙasar a shekarar 2015 daga Mali mai maƙwabtaka.
Tuni dai Burkina Faso ta ƙarfafa alaƙa da Rasha wadda take taimaka mata a fannin soji sannan ya yauƙaƙa dangantaka da Iran da Turkiyya, da kuma maƙotanta na yankin Sahel, wato Mali da Jamhuriyar Nijar, a yaƙin da take yi da masu tayar da ƙayar baya.