Gwamnan Kano da ke arewacin Nijeriya Abba Kabir Yusuf ya naɗa sababbin sarakuna masu daraja ta biyu a jihar.
Waɗanda aka naɗa su ne Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir Gaya, a matsayin Sarkin Gaya, wanda kafin naɗinsa shi ne tsohon Sarkin Masarautar Gaya da aka rushe.
Sai Alhaji Muhammad Mahraz Karaye, a matsayin Sarkin Karaye, wanda kafin naɗinsa shi ne Hakimin Rogo.
Sai kuma Alhaji Muhammad Isa Umar, a matsayin Sarkin Rano, wanda kafin naɗinsa shi ne Hakimin Bunkure.
Wata sanarwa da kakakin gwamnan na Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ta ce naɗin ya fara aiki nan-take.
"Yayin da yake musu murna bisa naɗin, Gwmana Abba K. Yusuf ya yi kira a gare su su kasance masu kiyaye al'adu da zaman lafiya da haɗin kan jama'arsu," a cewar sanarwar.
A ranar Talata ne Gwamna Abba ya sanya hannu kan sabuwar Dokar Masarautun Kano wacce ta ƙirƙiri Masarautun Gaya da Rano da Ƙaraye masu daraja ta biyu.
Gwamnan ya saya hannu kan sabuwa dokar ne 'yan sa'o'i bayan Majalisar Dokokin Jihar ta amince da sabuwar Dokar Masarautun a ranar Talata.
Sababbin masarautun za su ƙunshi wasu ƙananan hukumomi ne a ƙarƙashinsu, sai dai yawan ƙasashen Hakimansu bai kai na tsofaffin masarautun da aka rushe ba.
Sanarwar da Sanusi Bature ya fitar ta ce a yanzu "Masarautar Gaya za ta ƙunshi ƙananan hukumomin Gaya da Ajingi da Albasu ne kawai. Rano za ta ƙunshi ƙananan hukumomin Rano da Kibiya da Bunkure kawai, yayin da Ƙaraye za ta ƙunshi ƙananan hukumomin Ƙaraye da Rogo kawai."
Naɗa sabbin sarakunan na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da tirka-tirka kan dokar da gwamnatin jihar ta sanya wa hannu ta rushe masarautu huɗu na Gaya da Rano da Ƙaraye da kuma Bichi, da sauke Sarki Aminu Ado Bayero da kuma mayar da Sarki Muhammadu Sanusi na II kan sarauta.