Gwamnan jihar Kano da ke Nijeriya Abba Kabir Yusuf ya sanar da haramta duk wani taron jama'a da nufin gudanar da zanga-zanga a jihar.
Gwamnan ya sanar da ɗaukar matakin ne a wata sanarwa da kakakinsa Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ranar Laraba.
Sanarwar ta ce a matsayinsa na babban mai tabbatar da tsaro, Gwamna Abba ya umarci 'yan sanda, Hukumar Tsaro ta Farin Kaya da Jami'an Civil Defence da ke jihar da su kama, su ɗaure tare da kai kotu duk wani ko wata ƙungiya da aka samu tana zanga-zanga a titunan Kano.
Sanarwar ta ƙara da cewar gwamnan ya ɗauki matakin ne bayan ya samu bayanai da ke nuna cewa wasu 'yan siyasa na jam'iyyar adawa suna shirin tayar da hankali a jihar.
"Mun samu ƙwararan bayanan sirri da ke nuna cewa wasu jiga-jigan 'yan siyasa na jam'iyyar adawa a Kano sun kitsa ɗaukar nauyin zanga-zangar da ƙungiyoyin ɗalibai da na siyasa daga sauran jihohin arewa maso yamma za su gudanar domin tayar da hargitsi da sunan saukakken Sarkin Kano Aminu Ado Bayero," in ji sanarwar.
Kazalika sanarwar ta ja hankalin dukkan mazauna jihar da su ci gaba da gudanar da al'amuransu yadda suka dace a yayin da jihar ke samun lumana, kuma gwamnati za ta sanya idanu donkawar da duk wani yunƙuri na haddasa husuma a jihar Kano.
Tun bayan da majalisar dokokin jihar Kano ta yi kwaskwarima ga dokar masarautu tare da rushewa da sauke Sarakuna biyar da gwamnatin Abdullahi Ganduje ta ƙirƙira, sannan gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan dokar da ta dawo da Sarki Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano, jihar ta faɗa cikin zaman ɗar-ɗar.
A makon jiyar ne Gwamna Abba ya ba da umarnin kama Alhaji Aminu Ado Bayero saboda zargin yunƙurin tayar da tarzoma a jihar bayan ya shiga jihar cikin dare inda ya sauka a Gidan Sarki da ke Nasarawa.
Babbar Kotun Tarayya da Babbar Kotun Jihar Kano sun bayar da umarnin a fitar da Sarki Sanusi II daga gidan Sarkin Kano da kuma Aminu Ado Bayero da ke zaman fada a gidan Sarki na Nasarawa.