Mista Yevgeny Prigozhin ya shafe shekaru yana jagorantar rundunar sojin Wagner. Hoto/Reuters

Masu bincike a kasar Rasha sun ce gwajin kwayoyin halitta sun tabbatar da cewa Shugaban Wagner Yevgeny Prigozhin na daga cikin fasinjojin jirgin sama goma da suka rasu sakamakon hatsarin jirgin saman da ya faru a ranar Laraba.

Hukumar jiragen sama ta Rasha a baya dama ta wallafa sunaye goma na mutanen da ke cikin jirgin da ya fadi.

Sun saka sunan Prigozhin da Dmitry Utkin wanda shi ne na hannun daman Mista Prigozhin kuma wanda da shi aka kirkiro rundunar sojin haya ta Wagner.

“A wani bangare na binciken hatsarin jirgin sama a yankin Tver, an kammala gwaje-gwajen kwayoyin halitta,” kamar yadda kwamitin binciken na Rasha ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Telegram.

“Kamar yadda sakamakonsu ya bayyana, an tabbatar da dukkan mutanen 10 da suka mutu. Sun yi daidai da sunayen da aka bayyana da na cikin jirgin,” in ji sanarwar.

Jirgin dai ya yi hatsari ne kusan watanni biyu bayan da Prigozhin ya yi kokarin jagorantar wata kwarya-kwaryar tawaye kan sojojin Rasha.

Hukumomi har yanzu ba su bayyana takamaimai abin da ya jawo hatsarin jirgin saman ba

Reuters