Kwamitin wasu 'yan gwagwarmaya a ranar Talata ya bayyana cewa mutum 31 sun rasu sakamakon wani hari ta sama da sojojin Sudan suka kai a Wad Madani babban birnin Al-Jazira da ke Sudan kwanaki biyu da suka gabata.
An kari harin ne bayan sallar isha'i a ranar Lahadi a birnin da ke kudancin Khartoum kamar yadda Wad Madani Resistance Committee, wadda tana daga cikin ɗaruruwan ƙungiyar da ke bayar da agaji a ƙasar da yaƙi ya ɗaiɗaita, kamar yadda wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na AFP ya fitar.
Sun zargi sojojin da amfani da "bama-bamai na duro", inda suka ƙara da cewa fiye da rabin wadanda suka mutu har yanzu ba a san ko su waye ba yayin da masu aikin ceto ke tono gawarwakin da aka lalata.
Tun a watan Afrilun 2023 ake fafata yaƙi tsakanin sojojin Sudan da kuma rundunar RSF, inda yaƙin ya yi sanadin mutuwar dubban jama'a tare da raba miliyoyin jama'a da muhallansu, wanda adadin shi ne mafi girma a duniya.
Duka ɓangarorin biyu sun zargi juna da aikata laifukan yaƙi, daga ciki har da kai hari ba ƙaƙƙautawa kan gidajen farar hula da sace kayayyakin agaji.
RSF a nuna yatsa a kanta inda aka zarge ta da sace kayayyaki da yin ƙawanya ga ƙauyaku da cin zarafi ta hanyar lalata a Al-Jazira da kuma tsallaken Sudan.