Gomman mayakan kungiyar Islamic State West Africa Province (ISWAP) ne suka mutu sakamakon fashewar nakiyoyi a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya.
Lamarin ya faru ne ranar Litinin a kauyen Arina Masallaci da ke karamar hukumar Marte, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato wasu shugabannin kungiyoyin da ke yaki da ta’addanci suna bayyanawa.
Ganau sun ce wasu manyan motocin daukar kaya biyu ne makare da mayakan na ISWAP suka kama da wuta lokacin da suka tunkuyi nakiyoyin da aka binne a kan hanya a kauyen na Arina Masallaci.
"Motocin cike suke da mayakan kungiyar inda daya daga cikinsu ta taka nakiya abin da ya sa duka biyun suka kama da wuta kasancea ba su da nisa a tsakaninsu," a cewar Babakura Kolo.
"Mayaka kusan 50 ne suka mutu a cikin motocin biyu sannan da dama daga cikinsu sun jikkata," in ji Kolo.
Mayakan suna kan hanyarsu ta kai hari lokacin da lamarin ya faru da misalin karfe bakwai na safe, a cewar Ibrahim Liman, daya daga cikin shugabannin ‘yan bijilante da ke yaki da Boko Haram.
"Mayakan na (ISWAP) sun mutu da yawa. Wadanda suka mutu sun kai 50," a cewar Liman.
ISWAP, wadda ta balle daga cikin kungiyar Boko Haram a 2016 inda ta zama babbar kungiyar a yankin Tafkin Chadi, tana fafatawa da Boko Haram a yunkurin kwace iko da yankin.
"Mun yi amannar cewa su ne suka dasa bama-bamai da nakiyoyi a wasu lokuta da suka wuce domin dakarun tsaro su taka amma ga shi kaikayi ya koma kan mashekiya," kamar yadda Liman ya ce.