An tabbatar da mutuwar mutane da dama yayin da wata tankar mai ta yi bindiga a jihar Eungu ta Nijeriya ranar Asabar, kamar yadda hukumomi suka tabbatar.
Majiyoyi da dama sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa lamarin ya shafi motoci shida saboda ruɗanin da aka shiga lokacin da tankar fetur ɗin ta yi bindiga, yayin da take saukowa daga wata hanya mai gangara a wani babban titi mai cunkoso a jihar ta Enugu.
Shaidu da suka tura wa wakilin Anadoul bidiyoyin abin da ya faru sun ce an tabbatar da mutuwar mutane aƙalla 15, ciki har da yara uku.
Kwamandan Hukumar Kare Haɗura ta Ƙasa a jihar Franklin Agbakoba Onyekwere ya ce ya je wajen, amma bai bayar da adadin mutunen da abin ya shafa ba.
Tankar man ta kama da wuta ne ƙasa da mako guda bayan mutane 98 sun mutu yayin da wata tankar mai ta yi bindiga a jihar Naija.
Kamfani dillancin labarai na Anadolu ya ba da rahoton cewa, Nijeriya ta fuskanci hatsarin tankar mai 172 inda mutane 1,896 suka mutu tun daga 2009. Matsalar ta fi yin muni a 2024, inda jumullar adadin mutanen da suka mutu suka kai 266.
Tun daga lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya hau mulki a watan Mayun 2023, Nijeriya ta fuskanci hatsarin tankar mai 28, waɗanda suka janyo mutuwar mutane 468, abin da ya kai 15% na duka hatsarorin da aka fuskanta tun 2009.
Saboda damuwar da ya yi kan yawan matsalar da ake samu, a baya-bayan nan Shugaba Tinubu ya kafa wani kwamiti mai ƙarfi da aka ɗora masa alhakin lalubo hanyoyin da za a bi don kawo ƙarshen yawan hatsarin tankokin mai.
Ya kuma umarci jami’an tsaro da hukumar kiyaye haɗura su ɗauki matakin hana yawan bindigar da tankokin mai suke yi.