Hukumomi a Nijeriya sun tabbatar da mutuwar fiye da mutum 100 sakamakon gobarar da wata tankar mai ta yi a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin ƙasar.
Tankar ta tashi ne daga jihar Kano a kan hanyarta ta zuwa garin Nguru na jihar Yobe amma ta yi hatsari a yankin ƙaramar hukumar Taura ranar Talata da daddare.
Tun da farko, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Jigawa DSP Lawan Shiisu Adam ya ce mutum 94 ne suka mutu nan-take sannan fiye da 50 suka jikkata sakamakon gobarar da ta tashi bayan tankar man ta faɗi.
Ya ƙara da cewa lamarin ya faru ne yayin da mutane suke rige-rigen kwasar fetur daga cikin tankar, abin da ya haddasa gobara.
DSP Lawan Shiisu Adam ya ce: "A jiya Talata da misalin 11:30 na dare muka samu labarin hatsarin wata tanka da ta taso daga Kano za ta je Nguru. A lokacin da ta zo Taura kusa da Khadija University, sai motar ta ƙwace daga hannun direban hakan ya sa tankar ta faɗi.
"Sai mai ya riƙa malala yana shiga magudanar ruwa da kwatoci. Wannan dalili ne ya sa mutane sun ga banza ta faɗi suka fito suna ɗiban mai. A lokacin ne wuta ta tashi. A nan-take an samu mutum 94 da wuta ta ƙone su ƙurmus, sai kuma mutum 50 da aka ɗiba aka kai su asibitin garin Ringim inda suke karbar magani," in ji kakakin 'yan sandan.
Sai dai shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Jigawa Haruna Mairiga ya shaida wa manema labarai cewa mutum 97 sun "ƙone ƙurmus" a wurin da lamarin ya faru, yayin da mutum takwas suka mutu a asibiti.
Ana yawan fuskantar hatsarin mota a Nijeriya sakamakon tuƙin ganganci da rashin bin dokoki lamarin da kan haddasa asarar rayuka.