Gobara ta yi ɓarna a shahararriyar Kasuwar Ladipo da ke Mushin da kuma kasuwar Owode Onirin da ke kan titin Ikorodu a birnin Legas na Nijeriya, inda ta jawo asarar miliyoyin Naira.
Rahotanni daga kafafen yada labarai sun nuna cewa gobarar ta tashi ne da tsakar daren ranar Talata, inda ta yi saurin bazuwa cikin shaguna da rumbun adana kayayyaki da ke cike da kayan aiki da injina da kayayyakin gyaran ababen hawa da babura, da na'urorin lantarki na gida.
Daraktar hukumar kashe gobara ta jihar Legas, Margaret Adeseye, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta bayyana cewa, ba tare da bata lokaci ba aka tura jami’an agajin gaggawa daga cibiyoyin kashe gobara na Isolo da Bolade, da Alausa domin shawo kan gobarar.
Adeseye ta bayyana cewa jami’an kwana-kwana sun samu nasarar shawo kan gobarar duk da cewa sun fuskanci kalubale sosai wajen isa yankunan da lamarin ya shafa.
Sannan wata gobara ta sake tashi a kasuwar Owode Onirin, inda ta yi ɓarna da ƙona shaguna da dama waɗanda ke sayar da kayan ƙarafa.
A cewar Adeseye, jami’an kwana-kwana daga cibiyoyin kashe gobara na Alausa da Ikorodu sun isa wurin domin shawo kan lamarin tare da kashe wutar.
Ta kuma ƙara da cewa, ba a samu asarar rayuka ba a duk gobarar biyu, inda ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin tashin gobarar.