Shagunan da ke ɗauke da kayan abinci da na amfanin gida gobarar ta shafa./ Hoto: Nyseom Wike

Shaguna 40 suka ƙone yayin wata gobara da ta tashi a wata kasuwa da ke Abuja babban birnin Nijeriya.

Lamarin ya faru ne a kasuwar Kaura Modern Market da ke gundumar Kaura a Abuja.

Rahotanni sun ce gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 11 na dare a ranar Juma’a, lamarin da ya yi sanadin ƙonewar shaguna 40 da ke ɗauke da kayan abinci da kuma na amfanin gida.

Gidan talabijin na Channels a Nijeriya ya ruwaito muƙaddashin daraktan hukumar kashe gobara ta Abuja Amiola Adebayo yana tabbatar da lamarin inda ya ce matsalar wutar lantarki ce ta jawo wannan gobarar.

Ya ce lamarin ya kara tsananta ne sakamakon wani janareta da aka ajiye a cikin shagon da gobarar ta tashi.

Ya ce an ba su rahoton tashin gobarar ne da misalin 11:11 na dare amma sai da misalin 1:59 na dare aka kammala kashe gobarar tare da taimakon masu kashe gobara na Abuja da kuma na tarayya.

TRT Afrika da abokan hulda