Wani gini mai hawa biyu ya rufta a unguwar Kubwa da ke Abuja babban birnin Nijeriya.
Lamarin ya faru a ranar Asabar da misalin ƙarfe 7:00 na safe, kamar yadda waɗanda suka shaida lamarin suka tabbatar.
Gidan talabijin na Nijeriya NTA ya ruwaito cewa an ceto aƙalla mutum huɗu daga cikin ginin, amma duk da haka ana zaton akwai sauran mutane da ke cikin ginin.
Rahotanni sun ce tuni hukumomin bayar da agajin gaggawa da jami’an tsaro suka isa wurin domin gudanar da aikin ceto.
Ruftawar ginin na zuwa ne kwana guda bayan aƙalla ɗalibai 22 sun rasu sakamakon ruftawar ginin wata makaranta a birnin Jos na Jihar Filato.
Rushewar gine-gine ya zama ruwan dare gama gari a Nijeriya, ƙasar da ta fi yawan al'umma a Afirka, lamarin da ƙwararru suke dangana shi da rashin aiwatar da ka'idojin gini, da sakaci da kuma amfani da kayayyaki marasa inganci.
Aƙalla mutum 45 ne suka mutu a shekarar 2021 bayan da wani dogon bene da ake ginawa ya ruguje a gundumar Ikoyi da ke babban birnin tattalin arzikin Nijeriyar, Legas.