Hukumar sadarwar Ghana ta ce  sama da layin SIM miliyan 25 aka kammala yi wa rajista a fadin kasar. Hoto/NCA

Hukomomi a Ghana sun ce sun toshe layin wayar salula miliyan 6.1, wadanda ba su yi rajista da hukumar kula da harkar sadarwar kasar ba.

A cewar Hukumar Sadarwa ta Kasa, NCA, layukan da aka katse, masu su ba su kammala yin rajistar su ba, tun bayan soma rajistar layukan waya a watan Oktoban 2021.

Babban daraktan NCA, Joe Anokye, ya fada ranar Laraba cewa akwai kusan layuka miliyan 11 masu aiki, amma marasa rajista wadanda za a sauke su daga sabis bayan cikar wa’adin 31 ga watan Mayu.

Ya ce zuwa yanzu, sama da layin SIM miliyan 25 aka kammala yi wa rajista a fadin kasar.

Aikin yin rajistar wani bangare ne na kokarin hukumar NCA na kakkabe haramtattun ayyukan da ake yi ta amfani da layukan waya.

TRT Afrika