Ma’aikatar Tsaron Ghana ta saka haramci na wucin-gadi kan amfani da jirage marasa matuƙa na ɗaukar hoto a lokacin rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar a ranar 7 ga Janairun 2025.
Dokar haramcin ta shafi duk wani nau’i na jirgi maras matuƙi na ɗaukar hoto wanda ake amfani da shi domin nishaɗi ko kuma kasuwanci kuma zai yi aiki ne a dandalin Black Star da ke Accra babban birnin ƙasar.
Jami’ai sun bayyana cewa an ɗauki matakin ne domin tabbatar da tsaron baƙi da waɗanda aka gayyata da sauran jama’a.
Ma’aikatar ta jaddada muhimmancin bin doka da oda da kuma hana tashe-tashen hankula a yayin babban bikin.
Ana sa ran bikin rantsuwar shugaban ƙasar za ta samu halartar mutane da dama, inda aka samar da tsaro yadda ya dace domin tabbatar da an yi komai yadda ya kamata.
A cikin watan Disambar da ya gabata ne aka gudanar da babban zaɓen Ghana inda John Dramani Mahama ya lashe zaɓen shugaban ƙasar bayan kayar da babban abokin hamayyarsa Mahamudu Bawumia.