Shugaba George Weah tsohon dan kwallon kafa ne da ya tsunduma harkokin siyasa. /Hoto: Reuters

Shugaban Laberiya George Weah ya amsa shan kaye a hannun jagoran 'yan hamayya kuma tsohon mataimakin shugaban kasar Joseph Boakai a zaben da aka gudanar a farkon makon nan.

Boakai ya samu kashi 50.89 na kusan daukacin kuri'un da aka kidaya, a cewar sakamakon zaben da shugabar hukumar zabe Davidetta Browne Lansanah ta sanar ranar Juma'a. Weah ya samu kashi 49.11.

“Sakamakon zaben da aka sanar da daddare, duk da yake ba a kammala sanarwa ba, ya nuna cewa Ambasada Joseph Boakai ne a kan gaba kuma ba za a iya kamo shi ba. Don haka, mintunan da suka gabata, na yi magana da zababben shugaban kasa Joseph Boakaiinda na taya shi murna,” in ji Weah.

“A yayin da muke magana a kan sakamakon zaben, ya kamata mu sani cewa mutanen da suka yi nasara ta hakika su ne al'ummar kasar Laberiya,” a cewarsa.

Weah ya bayyana cewa gogayyar da aka yi a lokacin zaben ta fito da babbar barakar da ke tsakanin 'yan kasar.

An gudanar da zagaye na biyu na zaben ne saboda babu dan takarar da ya samu kashi 50 cikin dari na kuri'un da aka jefa a zagaye na farko ranar 10 ga watan Oktoba.

A zagayen farko, Weah ya samu kashi 43.83 yayin da Boakai na jam'iyyar Unity Party, ya samu kashi 43.44 na kuri'un da aka kada.

TRT Afrika da abokan hulda