Fadar Shugaban Nijeriya ta mayar da martani ga dan takarar shugabancin kasar na jam'iyyar PDP a zaben 2023 Atiku Abubakar kan sukar da ya yi wa Shugaba Bola Tinubu game da kamun ludayin mulkinsa.
Atiku ya caccaki Shugaba Tinubu ne a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X ranar Talata inda ya zarge shi da gazawa wurin jagorancin ƙasar.
Ya zargi shugaban ƙasar da sakaci da aikinsa da kuma yin tafiye-tafiye ƙasashen waje yayin da Nijeriya ke fama da rashin tsaro.
“Tinubu ya tsaya wasa yayin da Nijeriya ke neman nutsewa cikin kogin rashin tsaro,” in ji shi.
Sai dai sanarwar da Fadar Shugaban Nijeriya ta fitar ta ce “Zargin da Alhaji Atiku Abubakar ya yi wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na ƙin daukar matakin da ya dace a kan rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arziki ganganci ne.
“Kwanaki kadan bayan ya yi wa shugaban ƙasa ƙazafi a kan batun karbar lamuni na kamfanin NNPC Limited, bai kamata a ce a matsayinsa na dattijo a ƙasar ya yi irin waɗannan kalamai ba," a cewar sanarwar da mai taimaka wa Shugaba Tinubu na musamman kan watsa labarai, Bayo Onanuga ya fitar.
“Mun yi amannar cewa har yanzu Alhaji Atiku yana jin raɗaɗin shan kayen da aka yi masa a zaben da ya gabata ne, kuma a yanzu yana neman duk wani abu da zai kai wa Shugaba Tinubu hari da shi,” in ji sanarwar.
Ta ce Shugaba Tinubu ba ya yin wata tafiya ba tare da shaida wa ƴan Nijeriya inda zai je ba. “Ya faɗi tafiyarsa da ya yi ta ƙashin kansa zuwa Faransa tare da ranar da zai dawo.
“Kuma ko a Faransa ma Shugaba Tinubu na bin diddigin abubuwan da ke faruwa a gida sannan yana kan gaba wajen warware kowace matsala,” sanarwar ta ce.
Sanarwar ta bayyana irin ayyukan da ta ce shugaban ya ba da umarnin a yi kamar sanyawa a kamo masu hannu a kisa sarakunan gargajiya biyu na Jihar Ekiti da yadda aka yi nasarar kama masu satar mutane fiye da 139 a kewayen Abuja da Kaduna da Binuwa a cikin mako guda da ya wuce.
Sannan ta fadi yadda aka cewa mutum 154 daga hannun masu garkuwa da mutane a cikin ƴan kwanakin da suka wuce.
Fadar Shugaban Kasar ta kuma yi wani batu mai kama da gorantawa Atiku inda ta ce ko a makon da ya wuce Shugaba Tinubu ya amince da fitar da kudade na musamman har Naira Biliyan 50 don magance matsalar tsaro da ke damun Arewa Maso Gabashin kasar, yankin da Atiku ya fito.