Shugaban Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya Abdullahi Umar Ganduje ya roƙi gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf da ya bar jam’iyyar NNPP ya koma ta APC.
Ganduje, wanda shi ne tsohon gwamnan Kano da Abba Kabir ya gada, ya bayyana hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki na APC da aka yi a Kano a ranar Alhamis.
Shugaban jam’iyyar ya ce komawar Abba Kabir APC zai sa Jihar Kano ta zama jiha mai jam’iyya ɗaya.
Wannan kira na Ganduje na zuwa ne kusan mako guda bayan da Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ba shi shawarar cewa ya sasanta da jagoran NNPP Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, bayan da Kotun Koli ta tabbatar da nasarar Abba K Yusuf a matsayin gwamnan Jihar Kanon.
A ƙarshen taron, Ganduje ya sha alwashin jawo hankalin dukkan ƙananan jam'iyyu su koma ƙarƙashin jam'iyyar APC.
Ya kuma tabbatar da cewa APC za ta bai wa Abba Gida-Gida da magoya bayansa duk wata dama ta jin daɗin zama a jam'iyyar.
"A yanzu mun yi nasarar jawo hankalin wasu gwamnoni don su shiga APC. Nan ba da daɗewa ba wasu gwamnoni za su shigo jam'iyyarmu. To idan har za mu iya yin hakan a matakin ƙasa, me zai hana mu iya yi a matakin jiha?
"Hannayenmu a buɗe suke. Muna roƙon waɗanda ke son shiga jam'iyyarmu. Musamman, muna gayyatar gwamnan Kano da ya bar jam'iyyarsa ta NNPP ya koma APC.
“Muna kira gare shi. Mun yi alkawarin samar da yanayi mai kyau ga gwamnan da Jihar Kano ta yadda za mu samar da mabiya masu yawa.
"Wannan shi ne kwatankwacin yawan al'ummarmu tun da mu ne jiha mafi yawan jama'a a tarayya," a cewar Shugaban na Jam'iyyar APC.