Daga Maxwell Agbagba
TRT Afrika, Accra
A tsakiyar ƙasar Ghana, wani fasihin mawaƙi na tashen da ya zarci ƙananan shekarunsa. Ku gana da Kallai Nana Qwaachi,wanda cikin ƙauna ake kira da Fotocopy, ɗan shekara goma da haihuwa wanda ya samu kyaututtuka guda 25 a shekarun uku kacal.
Kyautar da ya samu ta baya bayan nan ita ce ta Gwarzon Sabon Mawaƙi na Shekara, inda cikin tunƙaho, ya ajiye ta a wani muhimmin waje a ɗakin mahaifinsa, wata sheda da ke nuna irin baiwar da yake da ita da kuma jajircewa.
Tafiyar Fotocopy a fagen waƙa ta fara ne tun yana ɗan shekara bakwai da haihuwa, yayin da ya gaji mahaifinsa Shedrach Nana Qwaachi, wanda fitaccen mawaƙin High Life ne a Ghana.
Yadda ya himmatu ya fi mahaifinsa shuhura a wajen waƙa, sai ya yi amfani da laƙabin "Fotocopy" domin ya nuna cewa shi ainihin juyen baiwar waƙa ta mahaifinsa ne.
Yin galaba kan shakku
Duk da shakkun da aka nuna tun farko, Waƙar Fotocopy ta farko, " Megye Me Dow," da aka saka a 2021, ta sace zukatan masu sauraro, abin da ya share fagen abin da zai zama samun ɗaukaka cikin ƙanƙanin lokaci.
A wata nasara gwanin sha'awa, Fotocopy ya haɗa hannu da shahararren mawaƙin Ghana, Shatta Wale domin yin waƙarsa ta biyu, wacce tuni an kalle ta fiye da sau miliyan ɗaya a tashar YouTube da kuma kallo dayawa a wasu kafofin.
Ku gana da Kallai Nana Qwaachi,wanda cikin ƙauna ake kira da Fotocopy, ɗan shekara goma da haihuwa wanda ya samu kyaututtuka guda 25 a shekarun uku kacal.
Ya ƙi ya yarda cewa ya zama wani abu, Fotocopy ya ci gaba harkarsa ta waƙa zuwa shekarar 2022 inda ya saki waƙa mai take "Tomorrow", wacce suka yi tare da shahararren mawaƙin Afrika ta Kudu, Uhuru.
Abin da ya bambanta Fotocopy da wasu ba baiwar waƙa da yake da ita ba ce kaɗai, face irin ƙwazon da yake da shi wajen yin waƙar da take da kyakkyawan tasirin kaɗai.
"Waƙa mai kyakkyawan tasiri kaɗai nake yi saboda iyayena sun gaya min ba sa son su raba ni da ƙuruciyata. Muddin ina yin waƙa, duk waƙoƙina za su zama masu kyakkyawan tasiri," Fotocopy ya jaddada cikin murmushi.
Karatu
Banda kiɗa da waƙa, Fotocopy ɗalibi mai himma ne ɗan aji Shida. Da yake haɗa sha'awarsa ta neman ilimi da kuma harkarsa ta waƙa, ya ƙaddamar da rangadin School Dey Bee a 2020. Shirin na da hadafin ƙarfafa wa yara guiwa su koma makaranta bayan matsalolin tsaiko masu nasaba da annobar Corona.
Cikin shauƙi Fotocopy ya bayar da shawara game da nema da bunƙasa baiwa da kuma neman ilimi. Ya shawarci matasa da kar su yi sakaci da neman iliminsu, yana bayyana tsarinsa na mayar da hankali kan karatu a ranakun mako da kuma mayar da hankali kan waƙa a ƙarshen mako.
Ya ce "Ina bibiyar baiwata a ranakun ƙarshen mako, a ranakun mako kuma, ina mayar da hankali a kan litattafaina. Idan yanzu kake gano baiwarka, ina roƙon ka, ka bai wa neman ilimi muhimmanci tukunna.
Tafiya da ɗaukaka
Samun ɗaukaka yana tattare da ƙalubalensa a gun Fotocopy. Tafiyar da ɗaukaka a irin waɗannan ƙananan shekaru yana da nasa ɗawainiyar da suka haɗa da hirarraki da kafofin watsa labarai masu yawa, da kuma hidimar magoya bayansa.
Duk da matsalolin, ya mayar da hankali a kan burinsa, yana godiya game da goyon bayan da yake samu duk da a wani lokaci yakan gundira.
Ya ce "Ina farin cikin yadda suke mini a makaranta amma wani lokaci suna zaƙewa. Wani lokaci idan na je makaranta, idan muna da wasanni ranar Juma'a, suna buɗe manhajar Bluetooth sai mu saka ɗaya daga cikin washegari, mu yi tattakin motsa jiki a zagayen lambun shaƙatawa. Sannan kuma, wani lokaci malamai suna ambatar sunana dayawa."
Makoma
Idan za a kintaci gaba, Fotocopy ya yi hasashen cewa shi ne zai zama babban mawaƙi a Ghana a cikin shekaru Goma masu zuwa. Muradunsa sun wuce Ghana, tare da burin haɗa guiwa da tauraron ƙasa da ƙasa kamar Davido, da Chris Brown da kuma Doja Cat.
Hasashen sana'ar Fotocopy na nuna cewa bai taƙaita ga nasarar waƙa kaɗai ba, har ma kyakkyawan tasiri a kan al'umma, yana haɗe baiwarsa da himma wajen neman ilimi da kuma zaburar da mawaƙa masu tasowa.
Yayin da matashin fasihin ke cigaba da kyakkyawan tasiri a fagen waƙa, duniya tana jira cikin zaƙuwa ta ga magaryar tuƙewar shaharar Fotocopy a harkar waƙa.