Hukumar da ke kula da gidajen yari ta Nijeriya ta bayyana cewa fursunoni fiye da 3,000 ne suke jira a yanke musu hukuncin kisa a kurkukunta da ke faɗin ƙasar.
Hukumar ta ce jimillar fursunonin da ake tsare da su a gidajen yarin Nijeriya baki ɗaya ya zuwa ranar 3 ga watan Satumba na 2024, sun kai mutum 84,741 waɗanda suka ƙunshi maza 82,821 da mata 1,920, kamar yadda jami'in hulda da jama'a na hukumar Abubakar Umar ya tabbatar wa kamfanin dillacin labarai na Nijeriya (NAN).
Kazalika, jami'in ya ce adadin fursunonin da ke jira a yi musu shari'a wato Awaiting Trial Inmates (ATIs) sun kai mutum 57,750 waɗanda suka haɗa da maza 56,303 da mata 1.447.
Sannan a ɓangare guda "Jimillar adadin fursunonin da suke jira a yanke musu hukuncin kisa ya kai mutum 3,590 waɗanda suka haɗa maza 3,517 da mata 73," in ji shi.
Sai dai hukumar ta ce babban ƙalubalen da take fuskanta a halin halin yanzu, bai wuce yawan fursunoni ba waɗanda galibinsu suke jiran shari'a, in ji jami'in mai magana da yawun hukumar.
Umar ya ba da tabbacin cewa hukumar na ɗaukar matakan da suka dace wajen shawo kan matsalar tare da tabbatar da gudanar da shari’a a kan lokaci ga waɗanda suke jiran hakan.
''Muna jinjina ga shiri da kuma goyon bayan da Ministan Harkokin Cikin Gida na Nijeriya, Dokta Olubunmi Tunji- Ojo ya bayar, wajen nasarar rage yawan fursunonin gidajen yarin ƙasar ta hanyar sakin mutane 4,063 waɗanda aka ba su zaɓin biyan tara ko diyya,'' in ji Umar.
Kan batun cunkoso a gidajen yari na ƙasar kuwa, hukumar ta ce tana kan gina sabbin wurare tare da faɗaɗa cibiyoyinta a cikin al'umma da kuma inganta kayayyakin aiki a kotu don tabbatar da an aiwatar da matakai daban-daban da za su taimaka wajen rage cunkoson fursunoni baya ga sakin da ake yi a-kai- a-kai.