Gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu Sokoto 

Al'ummar yankin Gobir a ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto sun ce matsalar tsaron da suke fama da ita na ƙara ta'azzara, tun tsawon fiye da wata guda da ya gabata.

Mutanen garin sun ƙara shiga cikin firgici da zaman ɗar-ɗar tun bayan kisan gillar da 'yan bindiga suka yi wa Sarkin Gobir na Gatawa Alhaji Isa Muhammad Bawa, a cewar Ɗan Iyan Gobir, Alhaji Hamisu.

Ya ce tun gabanin kisan Sarkin, 'yan bindiga sun yi garkuwa da mutum sama da 150 a ƙauyukan yankin Sabon Birni, amma ''ba lokaci ɗaya ba ne suka tafi da mutanen, sun ɗauki mutum 60 a rana guda, sai kuma wasu mutane 40, sai kuma ashirin da wani abu a rana daban, kuma kawo yanzu babu labarinsu,'' kamar yadda Ɗan Iyan Gobir ɗin ya shaida wa TRT Afrika Hausa.

Shi ma Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Sokoto mai wakiltar Isa da Sabon Birni Honarabul Aminu Boza ya shaida wa TRT Afrika Hausa cewa, 'yan bindigar sun sace mutum 53 tsakanin ranakun Juma'a zuwa Lahadi da suka wuce.

"Kafin mutuwar Sarki an ɗauke mana mutum 151, bayan mutuwar sarki an ɗauke mutum 53. A yanzu haka muna da mutum 204 a hannun 'yan binga," a cewarsa.

Ɗan Iyan Gobir Alhaji Hamisu ya ce ''har yanzu babu labarin waɗanda aka yi garkuwa da su, domin ko da 'yan uwansu da suka tara kuɗin biyan fansar da suka je kaiwa, 'yan bindigar kashe su suka yi, kusan mutane 12 aka kashe.''

''Babu abin da ke da haɗari irin rashin tabbas kan abin da zai iya faruwa da mutum, kullum muna cikin zaman fargaba,'' in ji Ɗan Iyan Gobir.

Rundunar 'Yan sandan jihar ta Sokoto a ta bakin mai magana da yawunta ASP Ahmed Rufai ta bayyana wa jaridar The Punch a ranar Lahadi cewa “Ba mu da wani rahoto a hukumance daga mazauna yankin kan wannan labari na garkuwa da mutane sama da 150.''

Ya ƙara da cewa “zan sake tabbatar muku da cewa rundunar 'yan sanda tana aiki ne tare da mazauna jihar don samun ƙarin haske kan lamuran tsaro don amfanin kowa.''

To sai dai Alhaji Hamisu ya ce duk da iƙirarin gwamnati da hukumomi ke yi na shawo kan matsalar, har yanzu mutane ba sa iya shiga Sokoto kai-tsaye ta hanyar Gobir, sai dai su yi zagaye ta jihohin Jamhuriyar Nijar uku, wato ta Madawa da Konni a shigo ta Ilela.

''Sannan wani abin takaici shi ne yadda 'yan ta'addan suke yi mana shaguɓe kan yadda suke cin karensu ba babbaka'' in ji shi.

Yana mai ƙari da cewa an san shugabannin 'yan bindigar da suke wannan aika-aika a yankin kuma an san garuruwan da suka fito, an kuma san iyayensu da kuma masu kai musu kayayaykin da suke buƙata, amma an kasa yin komai.

Aminu Goza ya ce mutanen yankin suna cikin mummunan yanayi, kasancewar kashi 90 na abin da suka mallaka ya ƙare wajen biyan kuɗin fansa. Don haka ne ma ya ce a yanzu haka mutanen ba su da abin da za su fanso 'yan'uwansu da shi daga hannun ɓarayin dajin, waɗanda ya ce suna cin karensu ba babbaka.

TRT Afrika