Fina-finan Afrika guda biyu sun samu shiga cikin fina-finan da za a fafata da su a bangaren fina-finan tarihi a gasar ta Oscar karo na 96.
Fim din “Four Daughters” na fitaccen mai shirya fina-finan nan na Tunisiya, Nadim Cheikhrouha da kuma “The Mother of All Lies” na darakta fina-finai na kasar Moroko Asmae El Moudir ne suka tsallake dukkan wasu matakan da ake bi har suka samu zuwa zagaye na karshe.
A yammacin Alhamis ne masu shirya gasar karrama fina-finai ta Oscar wato The Academy of Motion Picture Arts and Sciences suka bayyana fina-finai da sauran bangarori da za su fafata a rukunai guda 10 na gasar karo na 96.
Bangarorin da za su fafata a karramawar su ne, fina-finan tarihi wato documentary mai tsawo, da gajeran fina-finan tarihi, da fim din tarihi na duniya, da kwalliya, da waka da fina-finan ’yar tsana da fina-finan fada da sauti da hotuna.
Fina-finai 9 daga cikin 15 da suka kai zagaye na karshen duk na kasashen Turawa ne, uku daga yankin Asiya, sai daya daga Amurka.
Fina-finan da suka kai zagaye na karshe a fannin tarihi su ne:
Armenia, “Amerikatsi”
Bhutan, “The Monk and the Gun”
Denmark, “The Promised Land”
Finland, “Fallen Leaves”
Faransa, “The Taste of Things”
Jamus, “The Teachers’ Lounge”
Iceland, “Godland”
Italiya, “Io Capitano”
Japan, “Perfect Days”
Mexico, “Totem”
Moroko, “The Mother of All Lies”
Spain, “Society of the Snow”
Tunisiya, “Four Daughters”
Ukraine, “20 Days in Mariupol”
Birtaniya, “The Zone of Interest”
An sa rai sosai cewa fim din ‘Mami Water’ na C.J Obasi zai kai labari, wanda shi kadai ne dama fim daga Najeriya, amma bai kai zuwa zagaye na karshe ba.
Za a fara kada kuri’a ne a kan gasar daga Alhamis, 11 ga Janairun shekarar 2024, sannan a kamala a ranar Talata, 16 ga Janairun na badi.
Za a yi taron bikin karrama fina-finan na badi ne a ranar Lahadi 10 ga Maris a dakin taro na Dolby Theatre da ke birnin Los Angeles.