An kashe fararen-hula aƙalla 20 a biranen Sennar da Zalingei da ke babban birnin jihar Darfur ta tsakiya a Sudan, a wata arangama da aka yi tsakanin sojojin ƙasar da dakarun kai ɗaukin gaggawa Rapid Support Forces (RSF).
Jiragen yaƙin Sudan sun yi ruwan bama-bamai a sansanin Khamsa Dagaig da ke Zalingei, inda suka kashe mutane biyar tare da jikkata mutum uku a ƙarshen makon jiya, a cewar wata sanarwa da ƙungiyar farar-hula da ke sa ido kan sansanoni 'yan gudun hijira ta bayyana a ranar Lahadi.
Ƙungiyar likitocin Sudan da ke zaman kanta a yankin kudancin ƙasar, ta ba da rahoton cewa, kimanin mutane 15 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata, sakamakon luguden wuta da dakarun RSF suka yi ta yi a birnin Sennar a ranar Asabar.
"Munanan hare-hare kan fararen-hula sun janyo matsalar jinƙai, sakamakon harin da aka kai a sansanin 'yan gudun hijira, waɗanda tuni aka kai su asibitin koyarwa na birnin don yi musu magani," in ji sanarwa.
Gamayyar ƙungiyoyin agaji na haɗin gwiwa a El Fasher babban birnin jihar Darfur ta Arewa, ta faɗa a wata sanarwa da ta fitar cewa, dakarun RSF na ci gaba da luguden wuta a sansanin Abu Shouk na mutanen da suka rasa matsugunansu, inda aka harba harsasai huɗu cikin sansanin.
Kawo yanzu dai sojojin Sudan da dakarun RSF ba su ce komai ba kan lamarin ba.
An soma yaƙi a Sudan ne tun a watan Afrilun 2023, sakamakon saɓanin da aka samu tsakanin babban hafsan sojin ƙasar Janar Abdel Fattah al Burhar da kwamandan RSF Mohamed Hamdan Dagalo kan batun haɗa dakarun RSF wuri guda da Sojojin ƙasar.
Yaƙin ya haifar da mummunar matsalar jinƙai, inda aka kashe kusan mutane 18,800 tare da raba miliyoyi da matsugunansu, kuma ana ci gaba da fafatawa.