Macron ya ce an kawo karshen kawancen da ke tsakanin Faransa da Nijar/ Hoto: DPA

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce kasarsa za ta janye jakadanta sannan ta kwashe dakarunta daga Jamhuriyar Nijar nan da watanni kadan masu zuwa, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar wanda ya kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum.

"Faransa ta yanke shawarar janye jakadanta. Nan da awanni masu zuwa jakadanmu da sauran jami'an diflomasiyya za su dawo Faransa," a cewar Macron a hira da gidan talbijin na kasar ranar Lahadi.

Ya kara da cewa an kawo karshen kawancen soji da ke tsakanin kasarsa da Nijar don haka dakarun Faransa za su fita daga kasar "nan da makonni da watanni masu zuwa" inda rukunin karshe na sojojin zai bar Nijar a karshen shekarar nan.

Labari mai alaka: Sojojin Nijar sun umarci 'yan sanda su fitar da jakadan Faransa daga kasar

"Nan da makonni da watanni masu zuwa, za mu tuntubi sojojin da suka yi juyin mulki domin muna so a yi komai cikin lumana," a cewarsa.

'Har yanzu Bazoum ne halastaccen shugaban kasa'

Faransa tana da dakaru kusan 1,500 a Nijar wadanda suke yaki da kungiyoyin masu tayar da kayar baya a yankin Sahel.

Sojojin Nijar sun umarci jakadan Faransa Sylvain Itte ya fita daga kasar bayan da "ya ki amsa gayyatar" ma'aikatar harkokin waje don halartar wani taro da kuma "wasu matakai da Faransa ta dauka da suka ci karo da muradan Nijar".

Awanni 48 da aka ba shi ya fita daga kasar a watan Agusta sun wuce ba tare da ya fita ba, sannan Faransa ta ki amincewa da sojojin da suka yi junyin mulki.

Macron ya jaddada matsayin Faransa cewa sojojin "sun yi garkuwa" da Bazoum yana mai cewa a iya saninsu shi ne "halastaccen shugaba Nijar".

Sojojin sun yi masa juyin mulki ne saboda yana aiwatar da manyan sauye-sauye da kuma dalilai na kabilanci da matsoratan 'yan siyasa, in ji Macron.

AFP